Assalamu alaikum warahmatullahi ta'ala wabarakatuhu. Ya Allah Ka hada mu da alkairin da ke cikin wannan rana da ma na bayanta, ya Allah Ka kare mu daga sharrin da ke cikin wannan rana da ma na bayanta.
Alhamdulillah ala kulli halin, alhamdulillah ala hazal ni'ima(FAFCHAT).
Haqiqa wannan babbar ni'ima ce da Allah yasa wa su ma su hazaqa, kokari da kishin al'umma da kuma son kawo cigaba a duniya baki daya, su ka qirqikiri wannan manhaja. Allah yasa su cigaba da wannan kokari ba tare da gajiyawa ba , da kuma kallon ma su qalubalantar su akan rashin hujja da dalili. Ina fatan za su jurewa duk wani qalubale da zai kawo cigaban wannan manhaja ta FAFCHAT.
Sannan kuma ina Kira ga mutanen suyi amfani da wannan manhaja ta FAFCHAT wajen abubuwan da za su kawo ma al'umma cigaba, da kawunansu wajen yada dabi'u nagari, ilimi, kasuwanci da sauran.
A karshe ina yiwa wadanda suka kirkiri wannan manhaja ta FAFCHAT murna da wadanda suka shigo cikin ta (users). Allah ya hada mu da alkairin da ke cikin ta, ya karemu daga sharrin da ke cikin ta.